Iyayen al’umma sun nemi agaji

No comments

Mataimakin dagacin garin Danbare dake yankin karamar hukumar Kumbotso Mallam Sa’adu Suleman yayi kira ga masu iko da suyi hobbasa wajen ciyar da yankin su gaba

Mallam Sa’adu yace akwai wani matashi da basu san kowaye shi ba, yana gina azuzuwa a makarantar firaimare ta Danbare. Yayin da a share guda shima wani matashin da bai bayyanawa al’umma kan sa ba yake gina kwalbatoci, da zai taimakawa yankin kaucewa daga ambaliyar ruwa

Mataimakin dagacin yace akwai bukatar al’ummar yankin dake da halin aikata abin alkairai suyi koyi domin ciyar da yankin gaba

Sai dai kuma wakilin mu Tijjani Adamu yace yayi la’akari da irin tururuwa da masu garuwa keyi a lungunan Danbare, lamarin dake alamta matsalar karancin wadataccen ruwan sha

 

No Comments Yet.

Leave a comment

  • Mu na marhaba da masu sauraron mu.
  • Ku kasance da wannan tasha domin samun bayanin halin da birnin Kano ke ciki.
  • Constitutional Scholars To Sue Donald Trump Over D.C. Hotel And Other Businesses
close