Masu Hakan Kabari Sun Nemi Agaji

No comments

Masu ‘hakan kabari da kulawa da makabartar yankin ‘Dandolo dake yankin karamar hukumar Gwale sun yi kira ga gwamnati ta biya su kudaden alawus na wata-wata, da suka ce an kwashe tsawon lokaci baa biyan su

Wani jigo a kungiyar masu ha’kan kabari a makabartar Mallam Danjuma Labaran ne ya mika wannan bukata yayin da wakilin Dala fm Abubakar Abdullahi Soron Dinki ya kai musu ziyarada safiyar talatar nan

Danjuma Labaran ya shaidawa wakilin namu cewar ya fara aikin na ha’kar kabari tunda kuruciyar sa, wanda yace rabon su da karbar alawus daga gwamnati tun ¬†shekarar data gabata, wanda a lokacin anan biyan su naira dubu 3 a duk karshen wata

Daga nan Danjuma Labaran yayi kira ga mawadata dake da zuciyar tallafawa da su duba yiwuwar kawo musu dauki, da kayan aikin ha’kar kabari da kulawa dashi, duba da karatowar damunar bana

No Comments Yet.

Leave a comment

  • Mu na marhaba da masu sauraron mu.
  • Ku kasance da wannan tasha domin samun bayanin halin da birnin Kano ke ciki.
  • Constitutional Scholars To Sue Donald Trump Over D.C. Hotel And Other Businesses
close