Tukuntawa sun shiga ni ‘yasu

No comments

Unguwar Tukuntawa yanki ne dake cikin cikin kwaryar birnin kano, inda al uimmar sa kamar saura ke fama da matsalolin rayuwa

A wannan karon wakilin mu Tijjani Adamu ya bamu labarin cewa matsalar karancin ruwan sha na kara kamari a wannan yanki, inda ta kai jallin kananan yara na tafiya mai nisa kafin samun ruwan sha

Sanin kowa ne cewa tuni yara suka fara hutun makaranta, sai dai suna yin amfani da lokacin su ne wajen samar da ruwan sha ga gidajen su, ta hanyar ketarawa makotan unguwanni irinsu Sharada domin samun ruwan famfo

Wani matashi mai suna Nasiru Sabo Abubakar ya shaidawa Tijjani Adamu cewar baya ga matsalar karancin ruwan, yankin na Tukuntawa yana fuskantar lalacewar titunan da suka hada yankin da makota

Tijjani Adamu ya ruwaito cewar yanzu haka yara da dama ne ke ta ga ludaya a unguwanni dake makotaka da Tukuntawa, domin ganin sun samu ruwan sha

No Comments Yet.

Leave a comment

  • Mu na marhaba da masu sauraron mu.
  • Ku kasance da wannan tasha domin samun bayanin halin da birnin Kano ke ciki.
  • Constitutional Scholars To Sue Donald Trump Over D.C. Hotel And Other Businesses
close