Tarauni Stars zata barje da Eleven Tigers

No comments

Yan wasan kungiyar kwallon kafa na Enugu Rangers sun yi tutsun tattaki zuwa kasar zuwa kasar Zambia, domin  fafatawa a wasannin zakarun nahiyar Afirka dake gudana a Lusaka

Boren nasu ya biyo bayan sa’ba alkawarin biyan su alawus alawus na wasanni, koda yake tuni shugabannin kungiyar suka yi gaba domin share matsugunin yan wasan da a yanzu suka ki amincewa su yi wanan tattaki

A wani labarin kungiyar Katsina United ta amince ta biya tarar Naira Miliyan niyu da dubu ‘dari biyu da hukumar shirya gasar kofin kwararru ta kasa LMC tayi mata, biyo bayan wani farmaki da magoya bayan ta suka kaiwa yan wasan Enyimba

Shugaban kungiyar ta Katsina United Aminu Balele Kurfi ya ce sun yi amanna da wannan hukunci da LMC ta dauka akan kungiyar tasa, wanda ya bukaci magoya bayan da suke kai zuciya nesa

Anan kano kuwa da yammacin ranar juma’a kungiyar kwallon kafa ta Tarauni Super Stars zata kara takwarar ta Eleven Tigers dake unguwar Sauna Kawaji.

wakilin mu Tijani Adamuy ya bamu labarin cewa zaa fafata wasan ne a filin wasan kwallon kafa dake unguwar ta Sauna Kawaji, filin da zai karbi bakuncin Tarauni Stars

No Comments Yet.

Leave a comment

  • Mu na marhaba da masu sauraron mu.
  • Ku kasance da wannan tasha domin samun bayanin halin da birnin Kano ke ciki.
  • Constitutional Scholars To Sue Donald Trump Over D.C. Hotel And Other Businesses
close