wani hadari ya haddasa cunkoso a Dan-agundi

1 comment

Da misalin karfe 11 na safiyar yau Alhamis ne wani mota kirar marsandi C-class ta tunkuyi wani gini daya raba hanyar shigowa unguwar Dan Agundi

Wani mutum da lamarin ya faru akan idonun sa ya shaidawa Abba Isa Mohd cewar direban motar mai Suna Kabiru ya kwararo ne daga bangaren Gidan Murtala dake kan titin zuwa BUK, maimakon ya zabi hannun da zai bi sai kawai motar ta saki hannu ta tunkuyi tirken wutar kan hanya, sannan motar ta tayi ‘derere akan ginin daya raba hanyar biyu

Abba Isa ya shaida mana cewa motar ta samu matsala daga gabanta, yayin da direban ta Kabiru ya tsallake rijiya da baya

 

1 comment

  1. AKA YLAD45.

    Allah ya kiyaye ya kuma kare nagaba..direba kuma a rage gudu.

Leave a comment

  • Mu na marhaba da masu sauraron mu.
  • Ku kasance da wannan tasha domin samun bayanin halin da birnin Kano ke ciki.
  • Constitutional Scholars To Sue Donald Trump Over D.C. Hotel And Other Businesses
close