Gwamnati ki dube mu!

1 comment

Al’ummar yankin ‘yan kusa dake karamar hukumar Kumbotso sun roki gwamnati ta dubi lamarin ‘Ya’Yansu, na rashin makaranatar Firamare dake zame musu kadangaren bakin tulu

Mazauna yankin sun ce sun shafe tsawon shekaru bakwai(7) cur da wani gini mai azuzuwa 3 shima a bangaren dake makotaka mai suna Gadamar Fulani mai tazara, a cewar su daga nan har hazar yau gwamnati bata waiwayi lamarin su na ginin makaranta a matsugunin ta na din din din ba.

Wakilin mu Tijjani Adamu daya ziyarci yankin da sanyin safiyar yau ya iske yara na wasa a gaban wata rijiyar burtsatse, koda yayi musu tambaya kan ko suna zuwa makaranta? yaran sun amsa da cewa Eh! amma dai suna da matsaloli game da karatun nasu

Daga nan ne wakilin namu ya ‘karasa wajen iyayen su domin bin ba’asi, wanda suka shaida masa halin da suke ciki, daga nan kuma suka dauke shi zuwa wannan makaranta, wadda ginin ‘kasa ce kuma rufin langa langa, ajin ta kuma a bude yake hanhai babu koda kofa da zaa sakaya

Wakilin namu ya kuma ce jamian ‘yan sintiri sun bayar da nasu ofishin domin baiwa daliban sukunin samun ilimi, daga bisani idan dare yayi su kuma su kan yi amfani dashi domin gudanar da harkokin su na yau da kullum

1 comment

  1. aminu abdullahi ibrahim

    muna fatan gwamnati zata duba wannan koke nasu domin samar musu da isassun ajujuwa da isassun malamai domin cetosu daga halin da suke ciki, hakika barinsu haka babu makaranta ba karamar matsala bace kuma gashi wannan gwamnati tana ikirarin cewa ashirye take dan yin duk meyiyuwa wajen ganin ta bunkasa ilimi.

Leave a comment

  • Mu na marhaba da masu sauraron mu.
  • Ku kasance da wannan tasha domin samun bayanin halin da birnin Kano ke ciki.
  • Constitutional Scholars To Sue Donald Trump Over D.C. Hotel And Other Businesses
close