A KARO NA FARKO CIBIYAR KIWON LAFIYA TA GWMNATIN TARAYYA TA SAMU NASARAR AIKIN KASHIN BAYA.

Comments are closed

Cibiyar kiwon lafiya ta gwmnatin tarayya dake garin Makurdi a jihar Binuwai, ta ce ta samu nasarar gudanar da aikin tiyata na kashin baya a karo na farko.
Shugaban cibiyar kiwon lafiyar, Dakta Peter Inunduh ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Laraba, inda ya ce a karon farkon ne cibiyar ta fara gudanar da irin wannan aiki ga wasu masu fama da lalurar ciwon kashin baya su biyar a asibitin.
Ya ce wannan shine karo na farko da gwamnatin tarayya ta samar da kayan aikin kashin baya a asibitin, wanda kuma aka tura wasu daga cikin jami’an kiwon lafiyar zuwa kasar Masar tun a shekarar 2017, domin kara kwarewa a bangaren da ya shafi kashin baya da sauran kasusuwa.
Haka zalika, ya kuma ce a kalla an tura wasu likitoci 20 zuwa wasu sassan duniyar nan domin horas da su a fannin lafiyar.
Dakta, Peter ya kara da cewar, kayayakin aikin da gwamnatin tarayya ta samar tare da dakunan tiyata guda bakwai da kuma kwararrun likitoci shi ne ya baiwa asibitin na Makurdi damar aiwatar da aikin na kashin baya.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close