HUKUMOMI NA DAUKAR MAKATAN KARE YADUWAR CUTAR EBOLA A NAJERIYA.

Comments are closed

Hukumomi a filayen jiragen sama na kasar nan sun dauki tsauraran matakan kariya daga bazuwar cutar Ebola ta hanyar gyara na’urorin auna dumin jikin fasinjoji.
Jami’an kula da filayen jirage na kasar nan, sun dauki wannan mataki ne tun bayan samun bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya tace, mutane 45 ne suka kamu, inda 25 suka mutu sanadiyyar cutar a kasar ta Congo.
Mai magana da yawun hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, ta ce an farfado da na’urori masu auna zafin jikin dan’adam a dakin isowar baki na filayen jiragen saman kasar, wadanda aka girka tun a lokacin baya da aka samu bullar cutar a kasar.
Na’urar za ta yi kara domin ankarar da jami’ai da zarar dumin jikin mutumin da ke wucewa ta karkashinta ya zarta 38 a ma’aunin yanayin zafi.
Najeriya dai na iyaka ne da Kamaru, wadda ita kuma ke iyaka da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, inda aka gano bullar cutar ta Ebola.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close