KUNGIYAR AMNESTY TA ZARGI SOJOJIN NAJERIYA DA CIN ZARAFIN YAN GUDUN HIJIRA.

Comments are closed

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta zargi sojojin kasar nan da fararen hula ‘yan bindiga masu taimaka musu a yaki da kungiyar ‘yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar nan, da laifukan cin zarafi da hallaka mata ‘yan gudun hijira ta hanyar hana su abinci, har sai sun yi lalata da su.

A wani rahoto da kungiyar ta fitar a yau ta ce ta tattara shedar wannan cin zarafi ne ta hanyar tarin bayanai da ta samu da hirarraki da wadanda aka muzgunawar a sansanonin ‘yan gudun hijirar tun daga shekarar 2015.

Sa dai hukumomin sojin na kasar sun musanta zargin da rahoton ya bayar tare da cewa daman kungiyar ta Amnesty ta saba irin wadannan karerayi a kan jami’an tsaron kasar nan.

Kungiyar ta Amnesty International, wadda ta fitar da wannan sabon rahoto ta ce yawanci mata ‘yan gudun hijira da ke shiga cikin wannan ukuba, wadanda ake tsugunarwa ne a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke can wajen gari, a jihar Borno. bayan da rikicin ‘yan Boko Haram ya raba su da gidajensu, inda sojojin da fararen hula masu taimaka musu a yakin suke hana matan abinci da sauran kayan taimako, har sai sun yadda sunyi lalata da su.

Rahoton ya ce wannan ga wadanda suka tsira da ransu ke nan, domin ma wasu dubbai sun rasa rayukansu saboda rashin samun abinci a sansanonin. Abin da ke jefa mata ‘yan gudun hijirar a yanayi na sun yi gudun gara sun fada wa zago, ko gaba kura baya zaki a hannun wadanda ke ikirarin kare su, daga ‘yan Boko Haram.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close