MANOMA A KASAR INDIYA SUN FARA YAJIN AIKIN KWANAKI 10

Comments are closed

Manoma a kasar Indiya sun fara yajin aiki na kwanaki 10 daga yau Juma’a, 01 06 2018.

Manoman na neman Karin farashin kayayyakin amfanin su na gona da cikekken sassauci a lamani da basussukan da bankuna ke basu kana da kuma bukatar gwamnati ta biya sauran kudaden da ake bin kananan manoma dai-dai da abin da suke samu.

Masu yajin aikin sun dauki wannan mataki ne karkashin inuwar hadaddiyar kungiyar manoma ta kasar Indiya wato Rashtriya Kisan Mahasangh.

Manoma a jihohin yammacin kasar kamar Maharashtra da Gujarat da Rajasthan ta kuma takwarorin su daga bangaren arewaci irin su Punjab da Haryana da kuma jihohin tsakiyar kasar Madahyan Pradesh duka sun shiga yajin aikin ta hanyar datse zirga-zirga a lardinan.

Gidan talabijin na kasar sun nuna yadda manoman na Idiya suka bada hadin kai aga wannan mataki na yajin aiki a sassa daban daban na kasar.

Tuni hukumomin ‘yan sanda suka dauki matakan tabbatar da ganin cewa, yajin aikin bai yi sanadiyyar zubar da jinni ba.

‘yan sandan sun sha alwashin sanya kafar wando guda da duk wanda aka kama suna kokarin tada tarzoma da sunan yajin aikin.

Ministan ayyukan noma na kasar ta Indiya Gauri Bisen ya roki jama’ar kasar su kwantar da hankalin su.

Yanzu haka dai al’uma a manyan biranen na Indiya sun shagala wajen kayayyaki marmari da madara da kuma sauran kayan abinci suna adanawa, lamarin daya sanya tashin farashi tsakanin kashi 15 zuwa 30%

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close