NAJERIYA ZATA CI MORIYAR KASUWAR AFRIKA.

Comments are closed

A taron bita da kuma wayar da kan masana harkokin kasuwanci da yan kasuwa da ofishin cibiyar kula da harkokin kasuwanci na kasar nan ya shirya a jihar lagos,an bayyana cewa Nigeria zata ci moriyar kasuwar.

Babban daraktan cibiyar Ambassador Chidu Osakwe ne ya bayyana irin alfanun da Nigeria zata samu sanadiyyar kasancewarta cikin kungiyar harkokin kasuwanci ta afirka.ya kuma yaba da matakin da shugaban kasa muhammadu buhari ya dauka na kin sa hannu a yarjejeniyar kafa kungiyar harkokin kasuwancin har sai da ya samu amincewar yan kasuwa tare dam asana harkokin kasuwanci.

Ambassador Osakwe ya kara da cewa idan Nigeria ta shiga cikin kasuwar ta afirka babu shakka tattalin arzikinta zai fi na kasar Australia girma. Hakan ba zai tabbata ba har sai Nigeria ta taka rawar data kamata a kasuwar afirkan.

A yanzu haka alkalumma sun nuna cewa kasashen afirka na kasuwanci tsakaninsu ,da ya kai na dalar amurka biliyan daya da miliyan dari biyu kowacce shekara. amman da zarar an fara kasuwar, kasuwanci zai habbaka fiye da kasha hamsin daga cikin dari.

Injiniya Auwal Ibrahim , daya daga cikin shugabanin masu kananan masana`antu, ya ce sun amince Nigeria ta shiga kungiyar , kuma ya kamata gwamnati ta tashi ta yi wasu gyare-gyaren da zasu ba kasar nan damar rike matsayinta na kasancewa mai babban arziki nahiyar afirka.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close