TSOHON SHUGABAN KASAR NAN OBASANJO YA YI KIRA GA GWAMNATIN TARAYYA TA GWAGGAUTA DAUKAR MATAKIN SAHWO KAN MATSALAR TSARO

Comments are closed

Tsohon shugaban kasar nan Olusegun Obasanjo ya yi kira da akawo karshen yawan kashe kashen rayuka da ake fama da shi a fadin kasar nan.

Obasanjo na wannan kira ne a yayin da ya kai ziyarar jaje da ta’aziyya  ga gwamna Simon Lalong da al’umar jihar Plateu bisa kisan rayuka da aka yi a jihar.

A yayin da yake mika sakon ta’azyyarsa Obasanjo ya zargi gwamnatoci a matakai daban daban  wajen yin sakaci da kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma a fadin kasar nan.

Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta yi bincike domin ganin an gano musabbabin rikice rikicen dake faruwa wanda yayi sanadiyar asarar rayuka.

Obasanjo ya shawarci gwamnatin tarayya data hade kai da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da kuma kungiyoyin al’umma domin magance matsalar rashin tsaro a kasar nan.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close