WASU ‘YAN BINDIGA SUN KASHE FIYE DA MUTANE 20 A JIHAR TARABA

Comments are closed

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan wasu kauyukan Fulani biyar na karamar hukumar Lau a jihar Taraba.

Bayan kona gidaje da dukiya ‘yan bidnigar sun kuma yi awon gaba da shanu sama da dari biyar.

Rahotanni na nuni da cewa, lamarin ya jefa daruruwan mutane da suka hada da mata da yara cikin wani mawuyacin hali a jihar.

Al’amarin dai ya sanya al’umomin yankin da aka kai hare haren na kwarara gudun hijira zuwa Jalingo fadar jihar da kuma wasu yankunan dake makwabtaka da su,tuni direbobi suka daina bin hanyar Numan zuwa Mayo-Lope inda lamarin yafi shafa.

Shugaban kungiyar miyatti Allah Jauro Sahabi Mahmud ya bayyanawa manema labarai cewa, abun dake faruwa ya kazamta kuma yana bukatar daukin gwamnatin Tarayya.

Wasu ganau sun ce,”kawo yanzu fiye da mutum 20 aka yiwa jana’iza,yayin da rundunan yan sandan jihar ta bakin kakakinta,ASP David Misal wanda ya tabbatar da hare haren,ya ce sun kama mutum guda da ake zargi da hannau a cikin lamarin, amma yace mutane shida ne suka mutu, sanadiyyar harin.”

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close