Birnin Dala

Da Fatan Ku Na Tare Da Mu A Mita 88.5

Madalla Da Kulawa

Asma'u Sadiq (Baby-Nice)

Assistant Head of Production

Zainab Abdulrahman Mahmud

Head of Educational/Enlightenment

Muzzammil Ibrahim Yakasai (King Khan)

Head of News and Current Affairs

Nura Bello

Belnur?!

Fatima Muhammad Umar

Gwaggon Baba from Birnin Dala

Tijjani Adamu

Asst. Head of News and Current Affairs

Ghali Abdallah DZ

Sarki Ukasha

Head of Entertainment

Nasiru Salisu Zango

Manager Programmes

Ahmad Garzali Yakubu

Station Manager

A Cikin Labarai

AN KWANTAR DA GEOGE H.W BUSH A ASIBITI.

Comments are closed
An kwantar da tsohon shugaban Amurka, George H.W. Bush, a wani sashe da ake kula da masu cutar da ta yi tsanani a asibitin garin Texas, 'yan kwananki bayan rasuwar matarsa, A wata sanarwa da mai magana a madadin iyalan tsohon shugaban, Jim McGrath ya fitar, yace, "Tun ranar Lahadi aka kwantar da Bush Babba, mai
more

AN GUDANAR DA AIKIN IDO GA ‘YAN GUDUN HIJIRA

Comments are closed
Kwamatin shugaban kasa kan 'yan gudun hijira dake Arewa maso gabashin kasar nan, ya ce ya gudanar da aikin ido kyauta ga 'yan gudun hijira sama da 5000 a yankin. Shugabar kwamitin Amina Maibe ce ta bayyana hakan yayin ziyarar aikin idanu da ya gudanar a asibitin garin Maiduguri dake jihar Borno. Amina Maibe ta kara da
more

GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA YUNKURO.

Comments are closed
Kwamishinan Ilimn Kimiyya da Fasaha na Jihar Kaduna, Alhaji Jafaru Sani, ya bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Kaduna nan ba da jimawa ba za ta ci gaba da daukar malaman firamare a jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Kaduna. Jafaru Sani ya ce, " yanzu haka
more

AL’UMMAR UNGUWAR KURNA SUN KOKA.

Comments are closed
Al’ummar unguwar Kurna layin falwaya sun koka dangane da yunkurin gine masu makabartar da suke zargin wani mutum da jagoraran ta. Tun farko dai alummar yankin rana tsaka suka ga tarin wasu matasa da kayan aiki suna kokarin aza harsashin gini a makabartar lamarin da yasa mutanen yankin suka ce ba za su laminta ba. Sun kuma
more

BANKIN DUNIYA YA YI HASASHEN BUNKASAR TATTALIN ARZIKIN KASASHEN AFRIKA.

Comments are closed
Bankin duniya ya yi hasashen bunkasar tattalin arzikin kasashen Afrika da kashi 3.1 bisa 100 a wannan shekarar ta 2018 sakamakon farfadowar da suke samu bayan da suka fuskanci koma baya cikin shekaru ukun da suka gabata a sanadiyyar faduwar farashin kayayyaki a kasuwannin duniya. A cikin wani rahoton hasashe da bankin ya fitar game da
more

HUKUMAR LAFIYA TA DUNIYA WHO TACE ZA TA KASHE MAKUDAN KUDADE.

Comments are closed
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce za ta kashe makudan kudade har dala miliyan 178 a harkokin lafiya dake fadin kasar nan tin daga cikin shekarar nan da muke ciki har zuwa 2019. Wakilin mai kula da ofishin hukumar a kasar nan,Dakta Wondimagenehu Alemu ne ya bayyana hakan yayin taron wani hadin gwiwa da gwamnatin
more

FITACCEN LABARIN MAKO

Comments are closed
Sandar majalisa wata alama ce ta iko wacce idan babu ita ba za'a iya gudanar da zaman majalisa ba. Anshiga rudani acikin majalisar dattijai ta kasa a safiyar ranar laraba, 18,04,2018,  yayin da wasu yan daba suka kutsa kai cikin majalisar domin dawo da dakataccen dan majalisa OVIE
more

ANYI MUHIMMIN KIRA GA MATASA.

Comments are closed
Wani malami a sashen koyon illimin addinin musulunci na jami’ar Yusuf Maitama Sule, Dakta Ibrahim Ilyas, ya ja hankalin al’ummar musulmi da su mayar da hankali wajan gudanar da yin Sallar Asubahi bisa falalar dake tattare da ita. Dakta Ibrahim Iliyas, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da wakilin mu Umar Usman Gama a ofishin sa. Ya
more

WANI MATASHI YA RASA RANSA, YAYIN DA YAKE TSAKA DA AIKIN KAFINTA

Wani matashi mai suna John Ibrahim ya rasa ran sa,  ya yin da yake tsaka da aikin kafinta, a wani kamfani dake, Gunduwawa a karamar hukumar Gezawa.

Matashin John Ibrahim, ya rasa ran na sa ne sakamakon jan wutar lantar ki da ake zargin ta yi masa lokacin da yake tsaka da aikin.

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa da gidan radiyon Dala cewa ya taba wayar wutar ne da magwajin da yake auna katako a cikin rashin sani lamarin da yasa wutar ta fado da shi kasa daga saman benen da yake aiki.

Wakilin mu Abubakar sabo ya rawaito cewa ya tuntubi daya daga cikin jami’in gudanarwar kamfanin mai suna Adam A Bello wanda ya tabbatar da mutuwar matashin bayan sun kai shi asibiti.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.
  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.
  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.
  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.
  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.
close