HUKUMAR YAKI DA CIN HANCI DA RASHAWA EFCC,TA CE ILLAR DA RASHAWA DA CIN HANCI KE TATTARE DA ITA, TAFI CUTAR KANSA ILLA.

Comments are closed

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa illar da rashawa da cin hanci ke tattare da ita, tafi cutar kansa illa.

Magu ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a ofishin sa dake Abuja a jiya Ya ce “yadda cutar daji  ke ruguza lafiyar mutum sannan kuma a karshe ta halakashi baki daya, haka ita ma rashawa ke yiwa yan kasar nan irin wannan mumunar illar”

Ya kuma yi kira ga al’ummar kasar nan dasu kyamaci duk wani nau’I na cin hanci da rashawa sannan kuma al’umma su taimakawa hukumar wajen yaki da mummunar dabi’ar ta yadda talakan kasar nan zai samu yalwa da arziki mai dorewa a hannun sa.

Ya kara da cewa, suma kansu ‘yan jaridu dole ne sai sun shigo cikin hukumar ta hanyar tonawa da fallasa masu irin wannan dabi’ar ta cin hanci da rashawa.

Comments are closed.

  • Notice bar for all your custom notifications for your site visitors. Tweak them as you like using flexible options.

close