Za ta Kashe Biliyoyin Nairori Don Kammala Ayyuka Raya Kasa

Gwamnatin tarayya ta amince da kashe biliyoyin nairori domin kammala wasu ayyukan raya kasa a jihar Kano.

Ministan Samar da wutar lantarki ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola ne ya bayyana haka ga manema labarai yayin wata ziyarar duba aiki da ya kawo nan Kano.

Ministan wanda ya samu wakilcin daraktan kula da manyan titunan gwamnatin tarayya a ma’aikatar Engineer Busari Sikirulla Olalekan, ya ce; cikin ayyukan da gwamnati ta ware kudade domin kammala su, da fara su, sun hada da: kammala aikin gadar Tamburawa da ke kan titin Zaria wanda zai lashe naira biliyan daya da miliyan tamanin da tara.

Sauran sune: gyaran titin Kano zuwa Zari’a da raba titin Kano zuwa Wudil da aikin gadar western bye pass da aka yi watsi da shi shekaru goma da suka wuce da gina gadar Inna Kurum da raba titin Kano zuwa Katsina da kuma gina rukunin gidaje a unguwar Jaba

en_USEnglish
en_USEnglish