Asarar Miliyan Dari Takwas Da Sittin Da Takwas A Duk Shekara Inji NNPC

Kamfanin mai na kasa NNPC ya ce kasar nan na asarar naira miliyan dari takwas da sittin da takwas a duk rana sakamakon zurarewar iskar gas.

Shugaban kamfanin na NNPC Mai Kanti Baru ne ya bayyana haka yayin wani taron lakca da kungiyar Injiniyoyi masu aiki a bangaren man fetur suka shirya jiya a Abuja.

Ya ce adadin iskar gas da ake asara a duk rana ya kai ya samar da wutar lantarki mai karfin megawatts dubu biyar.

Anasa bangaren shugaban kamfanin bunkasa Albarkatun man fetur na kasa Aliyu Muhammed Gusau, ya ce wajibi ne a fito da sabbin dabaru na zamani domin magance matsalolin da ke sanya zurarewar iskar gas a kasar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish