Shirin Birnin Dala Ya Cika Shekara Daya.

A karon farko gidan Rediyon Dala FM ya shirya kasaitaccen taron murnar cika shekara daya da fara gabatar da wannan kayataccen wasan kwaikwayo mai farin jini na birnin Dala.

Dubun dubatar masoya wannan shiri na Birnin Dala ne, suka halacci wannan taro a ranar asabar,03,03,2018.

Kamar yanda aka tsara anfara taron ne da misalin karfe uku na yamma, yayin da jaruman da suke taka rawa cikin wannan wasan kwaikwayo suka shirya tsaf! Dan gamsar da masoyansu a zahiri ta hanyar gabatar da nuna wasu muhimman gidaje na musamman, dake kunshe cikin wannan wasan kwaikwayo dake nuni da zallar gudanarwar sarautar wasu masarautu guda uku; Masarautar yamma ta sarki Toro,wadda ke nuni da gudanarwar wata masarauta ta marasa addini,

sannan masarautar birnin Dala ta Sarki Ukasha dan sarki Kinana, jikan sarki Nawwasu,wacce ke nuna ainihin gudanarwar masarauta a kasar Hausa,

yayin da a karshe aka shirya nuna fitowar Masaurautar Mazugal ta Sarauniya Bilkisu, masaurautar dake da alaka da Larabawa.

Duk da mashirya wannan taro sunyi iyakar kokarinsu dan gabatar da dukkan abinda aka tsara, sai dai hakansu bai kai ga cimma ruwa ba, sakamakon yawan al’umar da suka taru dan shaida wannan taro, wanda hakan ba komai yake nunawa ba face, hakikanin farin jini, da kuma karbuwa da shirin yasamu a gurin masu sauraro. Babban abin burgewa ga wannan taro bai wuce yadda a cikinsa aka gabatar da wasannin masu burgewa dake nuni da Al’adun gargajiyar Bahaushe.

An kammala wannan taro ne da misalin karfe shidda na yamma,amma fitowa ta gagari yan wasan saboda yawan al’ummar dake muradin daukar hotunan tarihi dasu.

en_USEnglish
en_USEnglish