SANATA SHEHU SANI YA BAYYANA DALILAN DA SUKA YA FALLASA KUDIN DA SANATOCI KE KARBA A DUK WATA.

Dan majalisar dattawan kasar nan wanda ya fallasa yawan kudin da yan majalisu ke dauka a duk wata, Sanata Shehu Sani , ya bayyana dalilan da suka sa ya fallasa kudin da sanatoci ke karba a duk wata.

Dan majalisar yace “sama shekara 19 kenan da ake zargin yan majalisa na karbar miliyoyin nairori,amma kuma sun kasa fitowa su kare kansu tare da yiwa yan kasa bayanin ainihin kudaden da suke dauka a matsayin albashi na alawus”.

Sannan yace “ya yi maganar ne don sauran bangarorin Gwamnati kama daga alkalai, da Ministoci da Gwamnoni  da duk wadanda suke rike da madafun iko su bayyananawa yan kasa adadin kudin da suke samu da kuma abinda suke yi dasu.

en_USEnglish
en_USEnglish