HADA AURATAYYA TSAKANIN KABILU ABIN KOYI NE.

Sarkin Samarin Hausawan Jihar Oyo Alhaji Muhammadu Nasiru Yaro, ya bayyana auren diyar gwamnan Kano da na gwamnan jihar Oyo wanda ya gudana, cewa abin farin ciki ne wanda zai karawa ‘yan Arewa mazauna jihohin yamma tagomashi mussamman ma hausawa mazauna jihar ta Oyo.

Sarkin samarin yace, “Auratayya a tsakanin kabilu mabanbanta, ta taka muhinmmin rawar gani wajen kulla kyakayawar alakar kasuwanci da zamantakewa a tsakanin kabilun biyu,tare da ƙara samun fahimtar juna da zaman lafiya tare da sanin al’adun juna”.

Sarkin samarin hausawan na jihar Oyo yayi Kira ga al’umma su mayar da hankulan su akan alfanun da zai biyo bayan auren ba wasu kura-kuren da aka yi ba.

Sarkin samari Alhaji Muhammadu Nasiru Yaro yayi fatan samun kwanciyar hankali da zaman lafiya ga ma’auratan tare da fatan alakar ta zamo alkhairi ga al’umomin jihar Kano da na Oyo dama kasa baki daya.

en_USEnglish
en_USEnglish