AN BUKACI MATASA SU RUNGUMI SANA’AR KANIKANCI.

Kungiyar kanikawa ta kasa NATA reshen jihar Kano ta yi kira ga matasa  da kananan yara das u rungumi sana’ar kanikanci don gujewa zaman kashe wando  da kuma tsiratar da mutunci.

Shugaban kungiyar na reshen Sharada Mustapha Abdullahi ne ya furta hakan yayin taron rantsar da wasu ‘ya’yan kungiyar a unguwar Sharada dake karamar hukumar birni.

Mustapha Abdullahi ya ce shiga harkar sana’ar kanikanci zai baiwa matasa da kananan yara dammar samun aikin yi maimakon jiran aikin gwamnati.

Wakiliyar mu Zulfa’u Musa Yakasai ta rawaito cewa kungiyar ta NATA an kafatane tun shekarar 1919.

en_USEnglish
en_USEnglish