GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZATA FARA FITAR DA ZOBO KASAR WAJE.

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce, “Ta shirye tsaf domin fara safarar zoborodon da al’ummar jihar suke  nomawa zuwa kasar Mexico”.

Gwamnan jihar ta Jigawa wanda ya sami wakilcin mataimakinsa Barista Ibrahim Hassan Hadeja ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai jiya Laraba a ofishinsa.

Ya ce,” Wannan yunkuri ya biyo bayan amincewar da wasu masana suka yi kan cewa Zoborodo da manoman Jigawa ke nomawa na sahun gaba cikin  ingantaccen zobo da ake bukata”.

Mataimakin gwamnan ya kara da cewa,” Tuni dai wasu kasashe ciki harda kasar Mexico suka nuna sha’awarsu na siyan wannan zobo yadda suka amince da tallafawa manoman da ingantaccen iri da taki domin bunkasa noman na Zobo a fadin jihar”.

Haka kuma ya yi kira da manoman jihar dasu garzaya domin yin rijista tareda gujewa yin algus domin cin moriyarsu da bunkasa tattalin arzikin jihar baki daya.

en_USEnglish
en_USEnglish