HUKUMAR KASHE GOBARA TA JIHAR KANO TAYI KIRA.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Alhaji Saidu Mohammed,ya yi kira ga al’umma musamman ma ‘yan kasuwa da su rinka hanzarin sanar da hukumar kashe gobara a kan lokaci.

Alhaji Sa’idu ya bayyana hakan ne yayin da gobara ta kama a kasuwar ‘yan katako dake unguwar Rijiyar Lemo a safiyar jiya Laraba.

Ya ce samun rahoton gobarar  daga cibiyar hukumar dake unguwar Kurna ne ya sa hukumar ta yi hanzarin tura jami’an ta zuwa kasuwar don kashe gobarar.

Ya kuma bukaci ‘yan kasuwar da yin hanzari wurin sanarwa hukuma nan gaba idan hakan ya kara aukuwa, sannan ya shawarci ‘yan kasuwa da su tanadi abubuwan kashe gobora saboda riga kafi.

en_USEnglish
en_USEnglish