AL’UMMOMIN YANKIN MAIDUGURI SUN KOKA.

Al’ummomin yankunan Madagali, Michika da kuma Gwoza sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kai irin wannan ziyarar yankunan su.
Al’umomin yankin Suna ganin ziyarar zata bashi damar sanin halin da yankunan ke ciki sakamakon yawan kwashe masu matansu da ‘ya’yansu da Boko Haram suke yi.
Sun ce “Sau tari mahukuntan jiharsu basa bayyana irin matsalolin da suke ciki wanda suka ce Kodayaushe ‘yan Boko Haram suna iya shiga kauyukansu su kuma kwashe mutane su tafi da su”.
Mr Adamu Kamale dan majalisar wakilai na tarayya yace kawo yanzu akwai matansu da kuma daruruwan yara da yan Boko Haram suka sace,to amma har yanzu hukumomi a kasar nan basa maganarsu.

en_USEnglish
en_USEnglish