WANI MATASHI YA HAU KAN KOLOLUWAR ERIYAR GIDAN REDIYON KANO

Wani matashi mai suna isma’ila bege mazaunin unguwar shagari Quaters  layi na 7, ya hau kololuwar saman karfen eriyar tashar gidan Rediyon kano dake unguwar Tukuntawa,

a karamar hukumar Birni cewa ba zai sauko ba har sai gwamnan zamfara ya sauka daga matsayinsa na shugaban gwamnonin Arewa.

A wata takarda da matashin ya fitar yayin da yake kololuwar saman Eriyar cewa yana bawa yan uwa da abokan arziki, musamman mahaifiyarsa da ‘yayansa da kuma matarsa, dasu yi hakuri kan matakin da ya dauka.

Wakilinmu Tijjani Adamu ya zanta da wasu ganau wanda suka bayyana cewa matshin yace,”ba zai sakko ba har sai Gwamnan jihar Zamfara ya sauka daga mukaminsa”.

Yayin da wakilinmu  Ahmad  Rabi’u Jaen ya rawaito mana cewa jami’an hukumar kashe gobara sun bishi saman karfen Eriyar, kuma sun sami nasarar sakkowa dashi bayan daukar tsawon lokuta ana kokarin shawo kansa wanda tuni jami’an hadin gwiwa na tsaro su ka yi awon gaba dashi domin gudanar da bincike.

Sai dai kafin tafiya dashi dansa na cikinsa ya rungumeshi yana kuka yana kiran sunansa, Abba!Abba!! Abba!!!

 

en_USEnglish
en_USEnglish