A YAU ZA’A SAKI SAKAMAKON JARRABAWAR JAMB.

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta JAMB, Ta ce” yau ne dalibai masu bukata ta musamman za su zana jarabawarsu ta JAMB a wasu cibiyoyi biyar na jihohin kasar nan”.

Mai Magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya.

Ya ce “a cikin cibiyoyin akwai jihar Legas da Bennin da Enugu da Kano da kuma birnin tarayyar Abuja.

Ya kuma ce a yaune hukumar ta JAMB za ta saki sakamakon jarabawar dalibai miliyan daya da dubudari 3 da su ka zana jarabawar a fadin kassar nan”.

Sai dai kuma hukumar ta sauke jarabawa a wasu cibiyoyin, bisa samun cibiyoyin da ta yi ta na’urar kyamara ta CCTV da karbar na goro a hannun dalibai domin satar jarabawa da kuma yiwa ma’aikatan hukumar barazana.

 

 

en_USEnglish
en_USEnglish