GWAMNATIN JIHAR KANO TA AMINCE DA SAKIN NAIRA BILIYAN HUDU.

Gwamnatin jihar Kano ta amince da Naira biliyan 4 a matsayin kudin da za ta gina titin karkashin kasa da kuma gadar sama  titin zuwa Zaria da Silver Jubilee tare da titin gidan Zoo Wato Dangi.

Sanarwar ta fito ne a wata takarda mai kunshe da sa hannun kwamishinan labarai,matasa da kuma al’addu,Malam Muhammad Garba,” ya ce gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar zartaswa na jiha karo na 111.

ya ce aikin da gwamnatin za ta aiwatar na gina titunan, za su rage yawan cinkoso tare da hadura da ake yawan samu da kuma kawata jihar Kano da titunan zamani”.

Majalisar zartaswar, ta amince da dala dubu 36 a matsayin kudin da za a biya dalibai 18 kudin ayukan su na Project dake karatu a jami’ar El-Razi dake kasar Sudan,sai naira miliyan 39 a matsayin kudin zannuwan gado da kayayakin lafiya na makarantun sakandire 31 dake fadin jihar nan,sannan an ware naira miliyan dari 7 da 48 a matsayin kudaden gyara titin da ya taso tun daga Dawakin Kudu har zuwa Lahadin Makole dake karamar hukumar Dawakin Kudu.

Haka zalika majalisar ta kuma amince da Naira miliyan dari biyar da 88 a matsayin kudin gyarawa da kuma fadada titin Giginyu da kawo da kuma Eastern by pass dake karamar hukumar Nasarawa, sai naira miliyan dari biyu da 30 a matsayin kudaden da za a gyara asibitin sha ka tafi na Fagwalawa domin fadadashi.

 

en_USEnglish
en_USEnglish