DAN SAMA JANNATINNAN YACE YANA KAN BAKANSA.

Dan sama jannatin nan da ya hau kololuwar saman karfen gidan Rediyon Kano dake unguwar Tukuntawa mai tsawon mita sama da dari hudu,Isma’Ila Abdullahi Shabege, ya ce a shirye yake yayi fatali da fasahar sa tare da barin kasar nan har idan gwamnati ta yi watsi da fasaharsa wacce za ta samawa matasa aikin yi a fadin kasar nan.

A makon da ya gabata ne wato ranar juma’a Isma’ila Abdullahi Shabege ya hau saman kololuwar saman karfen wanda ya tayar da hankulan al’ummar jihar nan da ma kasa baki daya.

Ya ce tun hawan nasa saman kololuwar karfen, ya yi ne da hankalin sa bawai dimaucewa ya yi ba.Ya ce, “wasu basu fahimci yunkurinsa na hawa karfen ba, yayi ne ba domin kasar nan ta amfana wajan samawa matasa aikin yi.Shabege ya ce mataki na gaba shi ne ya tattara inasa- inasa ya yi waje har idan aka yi wasi da fasahar”.

en_USEnglish
en_USEnglish