HUKUMAR MA’AKATAR KASA DA SAFAYO TA FARA YIWA GIDAJE DA FILAYE RIJISTA.

Hukumar ma’aikatar kasa da safiyo ta jihar Kano ta fara aiwatar da rijistar gidaje da filaye da kuma gonaki dake fadin kananan hukumomi 44 na jihar nan.

Babban sakataren hukumar Alhaji Muhammad Yusuf Danduwa ne, ya bayyana hakan yayin kaddamar da fara rijistar a karamar hukumar Gwale a jiya.

Sanarwar ta fito ne a cikin wata takarda mai kunshe da sa hannun jami’ar hulda da jama’a ta hukumar,Sa’adatu Suleiman,ta ce, Gwamnatin jiha tare da hadin gwiwa da hukumar raya burane ta kasar Burtaniya DFID su ka kirkiri shirin tun shekaru uku da su ka gabata wanda a yanzu kuma gwamnatin jiha za ta daura a inda aka tsaya.

A nasa jawabin shugaban karamar hukumar Gwale,Alhaji Ishaq Diso kira yayi ga al’ummar yankin karamar hukumar ta Gwale dasu fito domin ganin sun yiwa gidajen su rijista tare da bada hadin gwiwa ga hukumar.

en_USEnglish
en_USEnglish