SHUGABAN ALKALAN KASAR NAN YA KOKA .

Shugaban alkalan kasar nan, Wilson Onnoghen, ya nuna damuwarsa kan gibin dake akwai tsakanin manya da kananan kotuna, musamman a matakan jihohi.

Onnoghen ya bayyana hakan ne yayin da yake bude taron alkalai abirnin tarayyar Abuja,ya ce gibin dake tsakaninsu shi ne sanadiyar rauni da kotunan ke fama dashi.

Mai Shari’a Onnoghen ya kuma ce idan ana son cimma nasara, dole ne a cike gibin dake akwai musamman akan ‘yancin cin gashin kai, da samar da kayan aiki da ma kudade a fannin shari’a a matakan jihohi.

Ya kara da cewa, jinkirin da ake samu wajen yanke hukunci a shari’un babban takaici ne.

Alkalin alkalan  Onnoghen ya ce, “Akwai bukatar sake duba kundin tsarin shari’ar kasar.

en_USEnglish
en_USEnglish