AN GANO DANSANDA ACIKIN YAN FASHI.

A jiya ne rundunar ‘yansandan jihar Kano ta yi holin wasu ‘yan fashi da makami da su ka shiga cikin gidan tsohon gwamnan jihar Jigawa a nan Kano.

A cikin wadanda rundunar ta yi holan su ya hadar da  wani kwararran dansanda mai suna Sani Danjuma  da nura ahmed da Abdullahi Ahmed, sai Abubakar zubair alais babayo, wadanda aka samesu da bindiga kirar  AK47 kamar yadda kakakin rundunar yan sandan jihar kano SP Magaji Musa Majiya ya bayyanawa manema labarai.

A hannu  guda kuwa  wani dansanda da ake zarginsa da yin uwa da makarbiya  kan wani koke da aka kawo masa na batan waya,inda yabi diddigi ya gano wayar tare da karbar zunzurutun kudi a hannun wanda aka sami wayar a hannunsa har naira dubu 15,ya kuma kashe maganar ba tare daya  sanarwa da ofishin yansandan da yake aiki ba.

Mai Magana da yawun rundunar yansandan jihar kano SP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni an kama wannan dansanda don cigaba da bincike tare da kwatowa da mai hakki hakkinsa.

 

en_USEnglish
en_USEnglish