KUNGIYAR BOKO HARAM TA SAKI YAMMATAN DAPCHI.

A sanyin safiyar yau Laraba ne ‘yan kungiyar Boko Haram suka saki ‘yammatan makarantar sakandiren dake garin Dapchi a jihar Yobe.

Daya daga cikin iyayen ‘yan matan ya shaida wa maneman labarai cewa, kungiyar Boko Haram ta rike daya daga cikin ‘yan matan sannan biyu sun mutu.

Ya ce, “da sanyin safiyar  yau ne wasu mutane suka mayar da ’yammatan garin na Dapchi a cikin motoci  suka ajiye su, suka tafi.

Ya kara da cewa iyaye na ta rububin zuwa domin dubawa da kuma dauko ‘ya’yansu.

Iyayen ‘yan matan Dapchi da mayakan Boko Haram suka sace sun ce, “Ba dukkansu aka saki ba.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da sakin ‘yan matan na Dapchi.

A watan jiya ne dai aka sace matan, lamarin da ya janyo cece kuce da sukar gwamnati da jami’an tsaron kasar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish