YANSANDA SUN CAFKE TSOHON SHUGABAN KASAR FARANSA

‘Yansanda sun kama tsohon Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, don yi masa tambayoyi kan zargin da ake masa na karbar makudan kudi don yakin neman zabensa, daga wajen tsohon Shugaban kasar Libya Mu’ammar Gaddafi.

‘Yan sanda kasar Faransa suna bincike kan zargin rashin bin tsari wajan samar da kudaden aiwatar da yakin neman zaben shugaban kasa da ya yi a shekarar 2007.

A baya ‘yansanda sun yi masa tambayoyi kan wannan bincike, Sai dai Mista Sakozy ya yi watsi da aikata hakan.

Tsohon shugaban kasar dai mai matsakaicin ra’ayi bai samu damar komawa kujerar mulki ba a 2012.

Majiyoyin shari’a sun ce ana yi masa tambayoyin ne a garin Nanterre, wani yanki da ke wajen yammacin birnin Paris.

Majiyoyin sun ce ‘yan sanda sun kuma yi wa daya daga cikin tsoffin ministocin Mista Sakozy kuma na hannun damansa Burayis Hotafiyu, tambayoyi a ranar Talata.

en_USEnglish
en_USEnglish