A YAUNE AKE BIKIN RANAR RUWA TA DUNIYA.

Wani rahoton majalisar dinkin Duniya da ya fitar ya ce yawan mutanen da ke rayuwa ba tare da tsabtataccen ruwan sha ba sun karu a duniya.

Rahoton ya ce yawan mutanen da ba su da tsabtataccen ruwan sha a duniya sun kai miliyan dubu dari takwas da arba’in da hudu.

Ya ce mutum guda cikin tara a duniya na rayuwa ne ba tare da tsabtataccen ruwan sha ba.

Binciken ya yi nazari ne kan yawan mutanen da suke samun tsabtataccen ruwan sha a gida ko kuma suke da halin samun ruwan a kasa da sa’a daya.

Ranar 22 ga watan Maris ta kowacce shekara rana ce da aka ware domin bikin ranar ruwa ta duniya da nufin wayar da kan al’umma game da muhimmancin tsaftataccen ruwan sha.

Kazalika rahoton ya yi gargadin cewa gwamnatoci da dama a nahiyar Afirka babu wani abin azo a gani da suke yi wajan samar da tsabtataccan ruwan sha, abinda ke jefa rayukan miliyoyin mutane cikin hadari.

Haka zalika rahoton ya ce mutum miliyan 57 a kasar nan ke fama da matsalar ruwan sha.

en_USEnglish
en_USEnglish