GWAMNATIN JIHAR KATSINA TA SALLAMI DAURARRU 165.

Kwamitin dake kula da cinkoso a gidan yari ya salami daurarru 165  dake babban gidan yari na jihar Katsina.

Sakatariyar  kwamitin, Leticia Ayoola Daniel ceta bayyana hakan yayin ziyara dasu ka kai gidan a jihar ta Katsina.

Ta ce a cikin mutane da kwamitin ya yiwa afuwa akwai wani dattijo mai shekaru 83 mai lalurar gani wanda ake zargin sa da kokarin yin fyade wanda ya shafe tsawon shekaru uku da wata 8 yana jiran a yanke masa hukunci.

Sannan mutane 49 an sake su ne bisa karamin laifi dasu ka aikata wanda gwamnatin jihar Katsina ta biya masu tarar da aka yi musu, sai wata mata da gwamnatin tarayya ta biya mata naira dubu 50 bisa tuhumar ta da ake da laifun cin zarafi.

en_USEnglish
en_USEnglish