KASAR AMURKA TA SAKE SAKAWA SUDAN TAKUNKUMI A KARO NA BIYU.

Kasar amurka ta saka  takunkumi kan wasu kamfanin mai a Sudan ta Kudu, a wani mataki na hana yadda kudaden da ake samu ke rura wutar yakin basasa a kasar ta Sudan ta Kudu.

Amurka ta ce daga yanzu kamfanoni za su bukaci lasisi na musamman gabanin samun fasaha ko kayan aiki ga wasu kwamfanonin mai sha biyar, da hukumomin gwamnati.

Ma’aikatar harkokin kasashen waje ta kasar tace gwamnatin Sylva Kiir wacce ta bayyana a matsayin gungun ‘yan cin hanci da rashawa.

Amurkar ta kara da cewa suna amfani da kudaden mai wajen sayan makamai, da bawa ‘yan bindiga dadi makamai, da kuma yin kafar ungulu ga zaman lafiya.

Ko a watan day a gabata said a kasara Amurka ta sanyawa kasar Sudan ta Kudu takunkumin sayen makamai.

 

en_USEnglish
en_USEnglish