MANOMMAN ALBASA SUN KOKA KAN YADDA SUKE FUSKANTAR MATSALA.

Kungiyar manoman albasa dake Karfi a karamar hukumar Kura sun bukaci gwamnati da ta samarwa da kungiyar rumfuna na din-din-din a kasuwar albasa dake yankin na karfi.

Mataimakin shugaban kungiyar, Alhaji Wadata ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da wakiliyar mu Zulfa’u Musa Yakasai a kasuwar ta Albasa dake karfi.

Ya ce rashin rumfuna na daya daga cikin abubuwan da yake janyowa sana’ar ta su koma baya.

Su ma wasu masu siyar da albasar sun koka cewa yawancin albasar tasu tana lalacewa da wuri bisa rana da take dukan albasar.

Wakiliyar ta mu Zulfa’u Musa Yakasai ta rawaito cewa,masu noman albasar sun kuma yi kira ga gwamnati da ta kara rage farashin taki domin samun sa cikin sauki.

en_USEnglish
en_USEnglish