KOTU TA AIKE DA WATA ‘YAR SIYASA GIDAN YARI A JIHAR KANO

Kotun majistrate mai zaman ta a rijiyar zaki karkashin mai shari’a Aminu Usman Fagge ta aike da ‘yar siyasar nan Hajiya Rabi Shehu Sharada gidan Yari bisa zargin ta da hana ma’aikacin gwamnati gabatar da aiki tare da tsoratarwa da cin mutuncin alkali wanda ya saba da sashi na 155 da 149 da 397 da kuma 114 na kundin penal code.

Kunshin tuhumar ya kara da cewa tun a ranar Talata da ta gabata ne Hajiya Rabi Shehu ta shiga gidan rediyon Rahama tare da fadin maganganun batanci ga alkalin kotun majistrate na rijiyar zaki bisa kan shari’ar da yake yi a kanta, Sai dai ta musanta zarge-zargen da ake yi mata.

Wakilin mu na kotu da ‘yansanda Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, kotun ta tura ta zuwa gidan yari domin cigaba da shari’ar a ranar 10 ga watan gobe.

en_USEnglish
en_USEnglish