KUNGIYAR MANOMA RESHEN JIHAR KANO TA YI KIRA GA MANOMA DA SU FARA AMFANI DA SABUWAR HANYAR AMFANI DA IRIN ZAMANI

Shugaban hadadiyar kungiyar manoma ta jihar Kano Faruk Rabi’u Mudi ya yi kira ga manoma dasu kama sabuwar hanyar yin amfani da irin zamani domin inganata harkar noma a damunar bana.

Faruk Mudi ya bayyana hakan ne yayin taron manoma daya gudana a Karfi dake karamar hukumar Kura a jiya Lahadi.

Ya ce har idan aka rungumi amfani da irin na zamani babu shakka manoman jihar nan za su samu amfani mai albarka a damunar bana.

Wakilin mu Aminu Ahmad Abbas ya rawaito cewa taron ya samu wakilcin manoma daga bangarori daban daban na fadin kasar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish