ANYI KIRA GA GWAMNATI DA TA MAYAR DA HANKALI WAJEN KULA DA LAFIYAR AL’UMMA MAI MAKON GINA GADAR SAMA

Wani kwararran lauya a nan Kano Barista Abdulkarim Kabiru Maude Minjibir, ya yi kira ga gwamnati da ta mai da hankali kan batun samar da lafiyar al’umma da kuma abin da lafiyar za ta ci maimakon mai da hankali a kan gina gadoji a fadin jihar nan.

Barista Abdulkarim Maude, ya bayyana hakan ne yayin shirin shari’a a aikace na gidan rediyon Dala FM.

Ya ce kundin tsarin mulki yayi maganar yadda za a gina dan Adam ta hanyar samar masa da lafiyayan abinci da kula da lafiyar sa.

Ya kuma kara da cewa, suma nakasassu suna bukatar kulawa ta musamman tare da samun walwala maimakon ace gwamnati ta mayar da hankalin ta kachokan kan gina gadar karkashin kasa.

en_USEnglish
en_USEnglish