KWATAMI NA NEMAN MALALE GEFEN WATA GADAR SAMA A JIHAR KANO

Rahotanni na nuni da cewar zuwa yanzu ruwan kwatamin dake malale a jikin gadar kasa ta sabon titin fanshekara na cigaba da malalowa, lamarin dake ciwa masu ababen hawa da mazauna gurin tuwo a kwarya.

Yayin wata ziyara da Gidan Radiyon Dala fm ya kai mun iske yadda masu ababen hawa ke tafiyar wahainiya lokacin da suke ratsa ruwan kwatar dake kwanciya a titin dake hannun Ja`en zuwa Dorayi.

Sai dai wasu mazauna Wurin sun bayyana cewar matukar damina ta sauka batare da an magance matsalar ba mai yuwuwa ne hanyar ta gagari masu ababen hawa da masu tafiya a kasa.

en_USEnglish
en_USEnglish