ALKALIN KOTUN MAJISTIRI DA KE RIJIYAR ZAKI YA SALLAMI ‘YAR SIYASAR NAN HAJIYA RABI SHEHU SHARADA

Kotun majistrat mai lamba 34 wadda take unguwar rijiyar zaki ta sallami Hajiya Rabi Shehu Sharada, wadda kotun ta tsare a gidan yari kwanaki biyar da suka wuce.

Barrister Abdul Adamu Fagge shine lauyan wanda yake kare Rabin, kuma shine ya umarci hajiya Rabi da ta bawa kotun hakuri kuma nan ta ke ta nuna nadamarta.

Tun a ranar asabar din da ta gabata ne dai mai shari`a Aminu Usman fagge ya aike da Rabi shehu sharada gidan yari bisa kalaman raina kotun da tayi a gidan radion rahama.

Mai shari`a Aminu Usman fagge yace ya yafemata amman bisa sharadin sai ta rubuta takarda na zata kasance mai kyakkyawan dabi`u anan gaba, tare da komawa gidan radion rahama don janyen kalamanta.

en_USEnglish
en_USEnglish