SHUGABAN HUKUMAR DA KE KULA DA GIDAJEN YARIN JIHAR KANO YA YI KIRA GA AL’UMMA DA SU DAI NA NUNAWA ‘YAN GIDAN YARI HALIN KO INKULA

Shugaban hukumar dake lura da gidajen yarin kano Alhaji Magaji Ahmed ya yi kira ga Al`ummar jihar nan dasu guji nunawa yan gidan yari halin ko in kula.

Alhaji Ahmed yayi wannan kiran ne lokacin da kungiyar yan jaridu masu dauko rahoto daga kotuna ta kai masa ziyara.

Shima sakataren kungiyar Mustapha Gambo Muhd ya roki hukumar da ta lamuncewa manema labarai su dinqa shiga gidajen yari don  gano halin da daurarru suke ciki.

en_USEnglish
en_USEnglish