GOBARA TAYI BARNA A KWALEJIN KIMIYYA TA JIHAR KANO.

wata gobara da ta tashi a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar kano ta kone shagunan sayar da abinci da sauran kayayyaki tare da haddasa asarar dukiya mai tarin yawa.

shaidun gani da ido sun ce gobarar ta tashi ne a daren jiya laraba bayan sallar magriba a bangaren masu sayar da abinci na makarantar da ke titin Yahaya Gusau.

wakilinmu Abba Isah Mohammad ya ruwaito cewa sai da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar kano suka zo wajen kafin aka samu aka kashe gobarar.

 

en_USEnglish
en_USEnglish