WASU ‘YAN BINDIGA SUN YI SANADIYYAR MUTUWAR MUTANE 6 A JIHAR KADUNA

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta tabbatar da mutuwar mutane 6, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Jama’a.

‘yan bindigar sun kai harin ne a yankin Bakin Kogi da ke masarautar Kanikon da ke karamar hukumar ta Jama’a, inda suka hallaka maza 4 da mata 2, tare da raunata wasu mutane 4.

Kakakin ‘yan sandan jihar kaduna Aliyu Mukhtar yace a halin yanzu, hadin gwiwar sojoji da ‘yan sanda suna kan farautar ‘yan bindigar.

A shekarar data gabata jihar Kaduna tayi fama da hare-haren ‘yan bindiga musamman a yankin Birnin Gwari, dalilin da ya sanya aka girke sojoji da ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro a yankunan da matsalar ta shafa.

en_USEnglish
en_USEnglish