AN BUKACI GWAMNATI DA TA RINKA BIYAN MA’AIKATA HAKIN SU

Wani lauya mai zaman kansa Barista Yakubu Abdullahi Dodo, ya yi kira ga gwamnati da ta rinka bawa ma’aikata hakokin su yadda yakamata maimakon barin sub a tare da basu kulawa ta musamman ba.

Barista Yakubu Dodo ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kamala shirin shari’a a aikace na nan gidan rediyon Dala a yau.

“Ya ce yin hakan yana ganin itace hanya ta farko da za a magance cin hancin da rashawa”.

“Ya kuma kara da cewa su ma al’umma suna da rawar takawa wajan magance cin hanci da rashawa”.

Barista Yakubu Abdullahi Dodo ya kuma gargadi al’umma dasu rinka zabar shugabannin da suka dace maimakon zaban jam’iyya domin yin hakan zai fidda al’umma daga matsalar ta cin hanci da rashawa.

 

en_USEnglish
en_USEnglish