WANI MATASHI YA RATAYE KANSA

Wani matashi mai suna Hafizu Sani dan garin Zango dake karamar hukumar Gezawa ya kashe kansa ta hanyar rataya.

Hafizu Sani mai kimanin shekaru 18 da haihuwa ana zargin ya kashe kan nasa ne bayan da ya rataye kansa a cikin dakinsa.

Mahaifin marigayin Malam Muhammad Sani, “ya ce shi kadai ne da namiji a wajansa a cikin ‘ya’ya hudu da ya Haifa, sannan ya kuma ce kafin rasuwar na sa dalibi ne a makarantar kimiya ta Gezawa sannan kuma mahaddacin al’qurani ne”.

Ya kuma yi addu’ar fatan Allah ya sauya masa da wani da wanda ya fishi.

Mai unguwar yankin Malam Yahaya Muhammad shaidawa gidan rediyon Dala cewa, “wannan shi ne karo na farko da wani mutum ya taba rataye kansa a unguwar ta Zango”.

Wakilin mu Naziru Abdullahi Wasai ya rawaito mana cewa, al’ummar yankin na Zango na cikin jimame bisa faruwar wannan lamari.

 

en_USEnglish
en_USEnglish