AL’UMMAR UNGUWAR DANBARE BASU DA WUTAR LANTARKI

Al’ummar unguwar Danbare Gabas dake karamar hukumar Kumbotso sun koka game da rashin hasken wutar lantarki da suke fama da shi a yankin na su sama da shekaru uku.

Al’ummar dai sun kokane yayin wata ziyara da suka kaiwa ma’aikatar raya karkara da Bunkasa rayuwar Alumma ta jihar Kano.

Da yake Magana da yawun mazauna yanki Ali Abdullahi Sani, ya kara da cewar baya ga matsalar Lantarki akwai matsalolin hanya , Ilimi Da lafiya wanda suke fama das hi tsahon shekaru.

Anasa jawabin komishinan raya karkara da bunkasa rayuwar alumma Hon Musa Iliyasu Kwankwaso, cewa yayi zasu duba koken mazauna yankin na danbaretare da daukar matakin magance shi.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa al’ummar yankin na Danbare gabas sun shawarci mazauna yankin da suke kokarin samar da magudanan ruwa..

en_USEnglish
en_USEnglish