AN BUKACI MATASA SU NEMI SANA’AR YI

Wani matashi anan Kano mai gudanar da sana’ar Kafinta, Abubakar Ya’u Mai jama’a ya ja hankalin ‘yan uwansa matasa da su dage wajen samun sana’ar da zasu dogara da kansu maimakon su zauna zuciyar su ta mutu.

Matashi yayi wannan jan hankalin ne yayin ganawarsu da wakilin mu Ahmad Rabi’u Ja’en.

Yace,” matukar matasa zasu dogara da kansu wajen samawa kansu mafuta ta hanyar sana’a to babu shakka zasu kasance ababan koyi anan gaba”.

Wakilin namu Ahmad Rabi’u Ja’en ya rawaito cewa matashin ya kuma gargadi matasa dasu dage wajen neman ilimin addini da na zamani baki daya domin ciyar da kansu gaba dama kasa baki daya.

 

en_USEnglish
en_USEnglish