YIN GILASHIN IDO NE MAFITA WAJAN MAGANCE HARARA GARKE GA YARA

Wani kwarraran likitan Ido dake asibitin kwarraru na Murtala Muhammad a nan Kano,Dakta Usman Mijin Yawa Abubakar, ya bayyana cewa rashin yiwa yara gilashi yayin da suke fama da ciwon ido shi ke haifar da cutar wurkilili ga rayuwarsu.

Dakta Usman Mijin Yawa, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakiliyar mu a yau.

Ya ce rashin yin gilashin idanu yayin da likitoci suka bukaci a yiwa yaran da suke fama da cutar, shi kan jawo musabbabin samun harara garke.

Ya kuma ce gilashin na taimakawa karfin ganin idanun yaran tunda tushe har zuwa girman su.

Wakiliyar mu Khadija Rabi’u Indabawa ta rawaito mana cewa,likitan ya kuma gargadi iyayen yara, dasu rinka gaggauta kai ‘ya’yan su asibiti yayin da suka fara ganin canji game da lafiyar idanun su.

 

en_USEnglish
en_USEnglish